Thailand: Ana alhinin mutuwar Sarki Bhumibol Adulyadej

Dubban mutane a Thailand sun saka bakaken kaya dan nuna alhini
Bayanan hoto,

Dubban mutane a Thailand sun saka bakaken kaya dan nuna alhini

Dubban mutane a kasar Thailand sun fito domin nuna alhini da kuma girmamawa ga Sarki Bhumibol Adulyadej wanda ya mutu a jiya Alhamis bayan ya shafe shekaru saba'in a kan karagar mulki.

Mutanen dai sun saka bakaken kaya a jikinsu inda suka jeru a fadar sarkin da ke Bangkok.

An kuma yi kasa-kasa da tutoci a kasar ta Thailand, bayan mutuwar Sarkin.

Yayinda aka fara zaman makoki na shekara guda a hukumance, an watsa tarihin rayuwar Sarkin a gidajen talabijin na kasar.

An kuma toshe hanyoyin da kafofin yada labarai na kasashen waje ke watsa shirye-shiryensu, ciki har da BBC.

Nan da wadansu sa'o'i za dauki gawar Sarkin daga asibiti zuwa wurin ibadarsu na Emerald da ke Bangkok.

Siwarnart Phranan, 'yar kasar ta Thailand, ta bayyana cewa yanzu a kasar kowa na cikin alhini.

"Babban rashi ne akayi wa al'ummar Thailand", injita, sannan ta kara da cewa, "Kuma za a ci gaba da tuna Sarkin a koda yaushe".