Samsung zai yi hasarar dala biliyan uku cikin watanni 6

Galaxy Note 7

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wayar na kama da wuta ne haka suddan saboda matsalar batur.

Kamfanin latironi na Samsung ya ce janye wayarsa ta Galaxy Note7 mai kamawa da wuta daga kasuwa zai zaftare masa ribar da zai ci da dala biliyan uku cikin watanni shidan da ke tafe.

Wannan ya biyo bayan sanarwar da kamfanin na kasar Koriya ta Kudu ya yi cewa ribarsa ta ragu da dala biliyan biyu a cikin rubu'in na uku na wannan shekara.

Ribar za ta ragu ne sakamakon hasarar kudaden da zai yi daga mai do masa da wayoyin da ya yi wa kiranye da kuma mayar wa abokan huldarsa miliyan biyu da rabi da suka mai do da wayar da kudadensu.

Kamfanin dai ya sanar da cewa zai dakatar da kera wayoyin na Galaxy Note7 bayan matsalar batur ta sa wasu daga cikinsu kamawa da wuta.