Nike zai dinka wa Chelsea kayan wasa na £900m

Chelsea na son kara yawan masu goyon bayanta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Chelsea na son kara yawan masu goyon bayanta

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta sanya hannu a wata yarjejeniya da kamfanin dinka kayan wasa na Nike inda zai dinka wa 'yan wasan kungiyar kaya.

Chelsea ta ce Nike zai dinka wa 'yan wasanta kayan da za su sanya a kakar wasa ta shekarar 2017 zuwa 2018, a yarjejeniyar sayen kayan 'yan wasa mafi girma da Chelsea ta taba kullawa.

A watan Mayu ne dai kungiyar ta ce za ta dakatar da sayen kayan wasa da take yi daga wajen Adidas kusan shekara shida da suka wuce.

A wancan lokacin rahotani sun ce kayan da za ta sya sun kai na £60m a duk kakar wasa har tsawon shekara 15, kodayake kungiyar ba ta tabbatar da rahotannin ba.

Nike zai dinka wa 'yan wasan babbar tawaga da 'yan makarantar samun horo da 'yan wasa mata da kuma magoya bayan kungiyar kaya.

Kungiyar ta Chelsea dai na son kara yawan masu goyon bayanta da kuma wadanda take huldar kasuwaci da su zuwa Gabashi da Kudu maso Gabashin Asia da kuma Arewacin Amurka.

Daraktan Chelsea Marina Granovskaia ya ce: "Mun yi amannar cewa Nike zai taimaka mana wajen bunkasa ayyukanmu da kuma matsayinmu a tsakanin manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya ."