Snapchat na shirin shiga kasuwar sayar da hannayen jari

Asalin hoton, Getty Images
Ana sa ran a karon farko hannayen jarin za su kai darajar $25bn.
Kamfanin Snap Inc, wanda ya mallaki manhajar aikewa da sakonni ta Snapchat, na dab da shiga kasuwar sayar da hannayen jari bayan da ya samu bankin da zai taimaka masa.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa bankunan Morgan Stanley da Goldman Sachs ne za su fara sayen hannayen jarin kamfanin.
Kazalika, za a sanya bankuna da dama cikin yarjejeniyar.
Ana sa ran a karon farko darajar hannayen jarinsa za ta kai $25bn.
Snapchat zai shiga kasuwar sayar da hannayen jarin ne a watan Maris na shekarar 2017 - inda zai kasance shafin sada zumunta mafi girma da zai shiga kasuwar tun bayan shigar Twitter a watan Nuwambar shekarar 2013.
Kimanin mutum miliyan goma ne a ke amfani da Snapchat wajen aikewa da sakonni a kowace rana, cikinsu har da sakonnin hotuna da bidiyo.