Jurgen Klopp ya fi kowanne kociya bajinta a Satumba

Klopp ya ce ya fi sha'awar cin wasa maimakon samun lambobin yabo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Klopp ya ce ya fi sha'awar cin wasa maimakon samun lambobin yabo

A karon farko kocin Liverpool Jurgen Klopp ya lashe kyautar kociyan da ya fi nuna bajinta a gasar Premier na watan jiya.

Haka kuma dan wasan Tottenham Son Heung-min ya zama dan nahiyar Asia na farko da ya fi bajinta a gasar Premier ta Ingila.

Liverpool ta kai mataki na dari bisa dari a watan jiya, inda ta sha gaban Leicester, Chelsea da kuma Hull bayan ta ci kwallaye 11.

Klopp ya ce, "na ji dadi da na yi wannan bajinta, amma na fi son cin wasa maimakon wannan kyauta."

Son Heung-min, mai shekara 24, ya zura kwallaye hudu a wasanni uku da Tottenham ta yi a watan Satumba.

Son ya ce, "Wannan shi ne mafarkin da na dade ina yi, wato na lashe kyauta. Ina so na yi ta lashe gasa."

Klopp, mai shekara 49, ya jagoranci Liverpool domin kai wa mataki na hudu a saman tebirin gasar Premier, inda suke bayan Manchester City da maki biyu.