Buhari ya yi raddi ga matarsa Aisha
Hirar BBC da Aisha Buhari na tayar da kura
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babban aikin matarsa shi ne dafa abinci, bayan da ta ce ba za ta sake mara masa baya ba idan har bai sauya salon gwamnatinsa ba.
Shugaban, wanda ke ziyara a Jamus, ya mayar da martanin ne cikin nishadi inda ya kwashe da dariya bayan da aka yi masa tambaya kan hirar da mai dakinsa ta yi da BBC.
Ya kara cewa, "Ban san jam'iyyar da matata take ciki ba, amma dai babban aikinta shi ne kula da gida."
Wannan ne dai karo na farko da shugaban ke mayar da martani ga matarsa tun bayan da aka fara ce-ce-ku-ce a kasar kan sukar da ta yi wa salon mulkinsa.
Mista Buhari ya ce "Na fi ta sanin yadda ake tafiyar da gwamnati".
Ita dai uwargidan shugaban na Najeriya ta gargadi mijinta cewa ba za ta goyi bayan takararsa a 2019 ba idan har al'amura suka ci gaba da tafiya a haka.
"Bai gaya min cewa zai tsaya ko ba zai tsaya ba tukunna, amma na yanke shawara a matsayina na matarsa, cewa idan abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka, to ba zan shiga cikin tafiyar ba.
"Idan har abubuwa ba su sauya ba, to ba zan fita na yi yakin neman zabe kamar yadda na yi a baya ba. Ba zan sake yi ba".
Za ku iya sauraran hirar da ta yi wannan bayani da sauran muhimman abubuwan da ta fada a shirinmu na Ganemi Mini Hanya a ranar Asabar.
Ta ce shugaban bai san mafi yawan mutanen da ya nada a cikin gwamnatinsa ba.
Ta kara da cewa wasu "'yan tsiraru" ne suke juya akalar gwamnati, inda suke zabar mutanen da ake bai wa mukami.

Asalin hoton, Getty Images
Mutane da dama na zargin gwamnatin Shugaba Buhari da rashin sanin alkibla
'Kan 'yan APC ya rabu'
Bayanin da Mista Buhari ya yi a lokacin da aka rantsar da shi cewa, "babu wanda zai juya shi, kuma shi na kowa ne," ya ja hankalin mutane sosai.
Sai dai kalaman na matarsa, da ma wadanda wasu masu kusanci da gwamnatin ke fada, na nuni da cewa lamarin ba haka yake ba.
A cewarta, "Shugaban bai san mutane 45 daga cikin 50 (alal misali) da ya nada ba, kuma ni ma ban sansu ba duk da cewa na shafe shekaru 27 tare da shi".
Aisha Buhari ta roki wadanda ta ce suna hana ruwa gudu da su tausayawa jama'a su daina abin da suke yi, sai dai ba ta kama sunan kowa ba.
Ta kara da cewa ba ta jin dadin yadda ake tafiyar da mulkin kasar.

'Yan Nigeria ka iya yi wa Buhari bore — Aisha Buhari
Wasu daga cikin tambayoyin da Naziru Mikailu ya yiwa Aisha Buhari:
- Zargin karkatar da kayan tallafi ga 'yan gudun hijira a Borno
- Su wane ne mutanen da suka kewaye Shugaba Buhari?
- Anya Shugaba Buhari ne ke jan ragamar gwamnatin kuwa?
- Kin yarda da abin da mutane ke cewa wasu 'yan tsirarun mutane ne ke tafiyar da gwamnati?
- Ko ya gaya mata cewa zai tsaya takara a zaben 2019
- Idan zai tsaya za ta goyi bayansa?
- Su wanene wadanda aka yi watsi da su a APC?
- Ya za ki kwatanta rayuwarku kafin ku hau mulki da kuma yanzu?
- Kamar sa'o'i nawa kike iya samu a rana tare da mai gidanki?
- Shin kin shaida masa cewa akwai matsala a tafiyar nan?
- Me za ta ce game korafin da ake yi cewa tana yawan tafiye-tafiye?
- A ina take samun kudaden da take gudanar da ayyukan ofis dinta?

Kada ku manta za ku iya kallo da sauraren hirar a talabijin da shafunmu na intanet, bbchausa.com