An sace wani dan Amurka a Jamhuriyar Nijar

Ba'amurken ya dade a yankin

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Maharan sun nufi kan iayakar kasar da Mali

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa wasu 'yan bindiga sun sace wani Ba'amurke mai aikin bayar da agaji sannan suka kashe masu gadinsa.

Lamarin dai ya faru ne a yankin Abalak da ke yammacin kasar.

Wani magajin gari a yankin ya ce masu satar mutanen sun je gidan Ba'amurken ne a kan babura da wata mota.

Ya kara da cewa an yi ta ba-ta-kashi da maharan kafin su sace shi su nifi kan iayakar kasar da Mali.

Rahotanni sun ce Ba'amurken ya shafe shekara da shekaru yana gudanar da ayyuka a garin, kuma ya iya yin magana da manyan yarukan yankin.