Swansea ta sa magoya bayanmu sun tsane mu —Wenger

Asalin hoton, Getty Images
Wenger ya ce Swansea ta janyo musu karan-tsana
Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce kashin da Swansea ta ba su a gidansu a kakar wasan da ta wuce ne ya kashe musu gwiwar lashe kofin Premier.
A cewarsa, hakan ya sa magoya bayansu sun yi matukar tsanarsu.
Kungiyar Swansea dai ta doke Arsenal da ci 2-1a watan Maris, sannan Manchester United ta buge su da ci 3-2.
Magoya bayan Arsenal dai sun caccaki Wenger bayan kungiyar ta sha kaye a hannun Swansea.
Kuma idan anjima ne ne kungoyoyin biyu za su sake yin karon-batta.
Wenger, mai shekara 66, ya ce "an tsane mu ne nan take bayan sun doke mu, kuma sai a hankali ne aka dawo da goyon bayan da ake yi mana."
Arsenal dai ta zo ta biyu a gasar Premier da ta wuce, tana da maki 10 a bayan Leicester.
Fitacciyar mai ci wa kungiyar wasa,Thierry Henry, ya ce bai taba ganin magoya bayan kungiyar sun yi fushi kamar yadda suka yi bayan Swansea ta doke su ba.
A wannan karon dai kungiyar za ta kara da Swansea ne bayan ta yi nasara sau biyar a jere.
Arsenal ce ta uku a saman tebirin gasar Premier, inda take bayan Manchester City, wacce ke ta daya a kan saman tebirin da maki biyu.