An zargi 'yan ta'adda da kashe sojoji 12 a Masar

Asalin hoton, AFP
Ana zargin wasu masu tsattsaurar ra'ayin addinin Islama da kashe sojojin Masar 12.
Jami'an tsaron Masar sun ce wadanda ake zargin 'yan masu gwagwarmayar kishin Islama ne, sun kashe sojoji 12 a wani hari da aka kai wani wajen da sojoji suka kafa shingaye a kan titi domin gudanar da ayyukan tsaro a Tsibirin Sinai.
An kuma jikkata sojoji takwas a harin da aka kai kusa da garin Beir al-Adb.
Wasu majiyoyin soji sun ce 'yan gwagwarmayar sun kaddamar da harin ne da bindigogi da wasu manyan makamai.
Wasu lokuta sojoji kan samu nasara kan 'yan bindigar, amma duk da haka maharan kan kai irin harin da suka kai a yau.
Wata sanarwar rundunar soji ta ce 'yan bindigar sun kai harin ne a kan wurin binciken ababan hawa dake kilomita takwas a gabashin Suez Canal.
A cewar rundunar sojin, an kashe goma sha biyar daga cikin maharan.
A baya-bayan nan dai ana samu karuwar tarzoma a Sinai.
Wata kungiya mai alaka da kungiyar IS ce ke jagorantar 'yan gwagwarmayar a yankin.