Gambia: Jam'iyyun adawa za su dunkule wuri guda domin karawa da shugaba mai ci

Jam'iyyun adawa zasu fitar da dantakara guda a Gambia
Bayanan hoto,

Jam'iyyun adawa zasu fitar da dantakara guda a Gambia

Jam'iyyun adawa a Gambia sun amince sun fitar da dan takara guda wanda zai kara da shugaba Yahya Jammeh a zaben kasar da za a yi a watan Disamba.

A cikin wata sanarwa da suka fitar bayan kammala wata tattaunawa da suka yi a Banjul, jam'iyyun sun ce sun ajiye bambamce-bambamcen da ke tsakaninsu a gefe guda sun zamo tsitsinya madaurinki daya.

Har yanzu ba a zabi dan takarar da zai wakilci jam'iyyun ba.

Shugaba Jammeh ya kasance yana mulkin kasar tun shekarar 1994.