Syria: Za a sake sabunta yarjejeniyar zaman lafiyar da aka rusa a watan da ya gabata

Ana tattaunawa akan sabunta yarjejeniyar zaman lafiya a Syria
Bayanan hoto,

Ana tattaunawa akan sabunta yarjejeniyar zaman lafiya a Syria

Sabunta yunkuri domin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria ya kankama a Switzerland bayan rushewar da yarjejeniyar da aka cimma a watan daya gabata ta yi.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai gana da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov.

Za kuma su hadu da ministoci da kuma jami'ai daga kasashen Turkiyya da Saudi Arabia da Iran da kuma Qatar.

Tun bayan rushewar yarjejeniyar ta baya, dakarun gwamnatin Syria da ke samun goyon bayan jiragen yakin Rasha su ka cigaba da kai hare-hare akan yankunan da yan tawaye ke rike da su a birnin Aleppo.