An yi mini magudi tun yanzu -Trump

Donald Trump

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mata da dama dai sun zargi Trump da taba jikinsu ba da yardarsu ba.

Donald Trump ya koka kan cewar yana fuskantar wani kamfe na bata suna mafi muni da aka taba gani a siyasar Amurka bayan da wasu matan suka kara zarginsa da yunkurin yin lalata da su.

Dan takarar na jam'iyyar Republican ya bayyana zarge-zargen a zaman karya tsagwaronta.

Duk da yake da sauran kusan watan guda kafin yin zaben, ya fadawa magoya bayansa cewa har an tafka magudi a zaben.

''A halin yanzu ana tafka magudi a wannan zaben. Wannan karairayi da kafafen watsa labarai ke watsawa ba tare da kawo shaida ko hujjar faruwar hakan ba, na gurbata tunanin masu zabe.''

Summer Zervos, wata tsohuwar 'yar takarar a gasar The Apprentice, ta ce Donald Trump ya nemi yin lalata da ita a otel din Beverly Hill a shekara ta 2007 yayin da ita kuwa dayar Kristin Anderson ta yi zargi cewa Trump ya ci mata zarafi a wani gidan rawa a birnin New York a shekarar 1990.

Sai dai Donald Trump ya ce duk matan da suka fito suka zarge shi da wannan abin ba su da ma kyawon da za su iya jan hankalinsa.