An kama masu yunkurin kai hari a masallaci a Amurka

Mutanen 'yan wata kungiyar ta'addanci ne mai suna The Crusaders

Asalin hoton, POLICE PHOTO

Bayanan hoto,

Mutanen 'yan wata kungiyar ta'addanci ne mai suna The Crusaders

An tuhumi wasu mutum uku da yunkurin kai harin bam kan wasu 'yan gudun hijirar Somalia da masallacinsu da ke jihar Kansas ta Amurka.

Mutanen su ne Curtis Allen, mai shekara 49 da Gavin Wright, mai shekara 49 da kuma Patrick Eugene Stein, mai shekara 47, wadanda suka tara bama-bamai da wasu abubuwan fashewa da zummar kai wa 'yan Somalian hari, in ji ma'aikatar shari'a ta kasar.

Jami'an tsaro sun ce mutanen 'yan wata kungiyar 'yan ta'adda ce mai suna the Crusaders.

An yi zargin cewa sun kitsa kai harin ne ranar tara ga watan Nuwamba, kwana daya kafin zaben shugaban kasar.

Masu shigar da kara sun ce mutanen da ake zargin sun yi shirin tayar da bama-baman ne a gidan da 'yan Somalia 120 ke zaune ta hanyar ajiye motocin da bama-baman ke ciki a kofar gidan.