Na yi murna da gayyata ta Hollywood— Rahama Sadau

Rahama Sadau
Bayanan hoto,

Rahama Sadau

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa a Najeriya wacce aka kora daga Kannywood, Rahama Sadau, ta ce dai ta ce ta ji matukar dadin gayyatar da mawakin nan na Amurka, Akon da wani mai shirya fina-finai na Amurkan suka yi mata.

A kwanakin baya ne Kannywood ta kori Rahama Sadau saboda an nuno ta, ta rungumi mawaki Classiq a wata waka da mawakin ya fitar.

Mutane da yawa sun yi ta mayar da martani daban-daban game da wakar da kuma korarta da aka yi.

Amma yanzu a shafinta na Tweeter, Rahama Sadau ta ce ta ji dadi sosai bisa gayyatar da Jeta Amata da Akon suka yi mata domin ta halarci wurin da suke hada sabon fim dinsu na Hollywooddadin.

Bayanan hoto,

Shafin Tweeter na Rahama Sadau

Tayin Hollywood da aka yi mata

Fitaccen mawakin Amurka, Akon, ya gayyaci Rahama Sadau zuwa birnin Los Angeles domin ya karfafa mata gwiwa bayan korar da aka yi mata daga Kannywood.

Shi ma shahararren mai shirya fina-finan Hollywood, Jeta Amata, ya gayyaci fitacciyar 'yar wasan zuwa Amurka domin ta taka rawa a fina-finan na Hollywood.

Mutanen biyu dai sun yi wannan gayyata ne a shafukansu na Twitter.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Akon ya shahara a fagen waka

Akon, wanda cikakken sunansa shi ne Aliaume Damala Badara Akon Thiam, mawaki ne kuma jarumin fina-fina, wanda ya girma a kasar Senegal.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce "Ina shaukin haduwa da ke [Rahama) a LA [ Los Angeles]. Ya kamata mu karfafa gwiwar mata sanna mu taimaka musu domin su ci gaba. Zaunawa tare da su ya fi a yi watsi da su."

Shi kuwa Jeta Amata cewa ya yi, "Muna shirin tarbar daya daga cikinmu [Rahama] a Hollywood!"

Asalin hoton, FINESSE ENTERTAINMENT

Bayanan hoto,

Ba wannan ne karon farko da take jawo ce-ce-ku-ce ba

An kori Rahama Sadau daga Kannywood ne saboda rungumar da ta yi wa wani mawaki mai suna Classiq a bidiyon wakar da ya sanya ta a ciki.

Batun dai ya janyo ce-ce-ku-ce, lamarin da ya sa ta nemi gafara, kodayake ta ce abin da ta yi din "ba laifi ba ne" a tsarin sana'arta.