Cikakkiyar hirar BBC da Aisha Buhari

Cikakkiyar hirar BBC da Aisha Buhari

Mai dakin Shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta ce wasu 'yan tsirarun mutane sun mamaye gwamnatin mijinta, Shugaba Muhammadu Buhari, inda suke hana ruwa gudu.

A wata kebantacciyar hira da ta yi da BBC, Misis Buhari, wacce ba ta bayyana sunayen mutanen ba, sai dai ta ce 'yan Nigeria sun sansu kuma tana tsoron boren da za su iya yi.

Aisha Buhari ta kara da cewa shugaba Buharin ya yi watsi da wasu 'ya'yan jam'iyyar APC wadanda suka sha wahala da mijin nata a lokacin gangamin yakin zabe.

Sai shugaba Buhari ya yi mata raddi, yana mai cewa babban aikinta shi ne dafa masa abinci da gyaran dakinsa.