Chelsea ta lallasa Leicester da ci 3-0

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta taka rawar gani
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta doke takwararta mai rike da kofin Premier na Ingila da ci 3-0 a karawar da suka yi ranar Asabar.
Tun a minti bakwai na farkon wasan Chelsea ta taka rawar gani inda Nemanja Matic ya zari kwallon da Eden Hazard ya tunkudo ta da kansa, ya mika wa Diego Costa wanda ya zura ta a ragar Leicester.
Hazard ne ya zura kwallo ta biyu bayan ya yi wa Kasper Schmeichel wayo inda ya zagaye shi.
Victor Moses ne ya zura kwallo ta uku.