Barcelona ba kanwar lasa ba ce —Guardiola

Sau uku Pep Guardiola yana jagorantar Barcelona wajen lashe kofin La Liga, yayin da ya shugabance ta wajen lashe kofin zakarun turai sau biyu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sau uku Pep Guardiola yana jagorantar Barcelona wajen lashe kofin La Liga, yayin da ya shugabance ta wajen lashe kofin zakarun turai sau biyu

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce Barcelona kungiya ce mai murza leda kamar da aljanu kuma mai yiwuwa ita ce za ta mamaye wasan da za su fafata ranar Laraba.

Dan kasar ta Spain ya lashe kofin Turai a lokacin yana dan wasa da kuma sau biyu a lokacin da yake kocin Barcelona.

Guardiola zai jagoranci City zuwa Nou Camp inda za su gwabza a gasar cin kofin zakarun turai, sane da cewa akwai jan aiki a gabansu.

Ya ce, "Barcelona na da hanya ta musamman ta murza leda. Suna yin wasa kamar aljanu."

Guardiola ya ce za a shafe tsawon lokaci kafin wata kungiya ta yi nasara irin wacce Barcelona ta yi.

A cewarsa, "A shekara goma da suka wuce, ko kuma ma shekara 50, Barcelona ta mamaye fagen kwallon kafa. Ina son yadda suke taka leda."

Guardiola ya kara da cewa Barca "Na da 'yan wasa uku masu ban mamaki, wato Lionel Messi, Luis Suarez da kuma Neymar."