Dan bindiga ya halaka 'yan Shi'a 32 a Bagadaza

Iraq Shi'a attack

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An kai harin ne a wani tanti, inda 'yan Shi'a suka taru

Akalla mutane talatin da biyu ne suka mutu lokacin da wani dan kunar bakin wake ya kai hari cikin taron mabiya akidar Shi'a a Bagadaza, babban birnin Iraki.

Wasu mutanen fiye da sittin sun jikkata a harin, wanda aka kai a wani tanti dake cikin wata kasuwa mai cinkoson jama'a a wata gunduma dake arewacin birnin.

Kungiyar IS ta dauki alhakin kai harin.

Musulmai 'yan Shi'a da yawa ne ke taron jimamin kashe jikan Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW) lokacin da harin ya auku.

Rahotanni sun ce dan kunar bakin waken ya tayar da bom din dake jikinsa ne a lokacin cin abincin rana, yayin da mutane da yawa suka taru.

A cikin wannan shekarar, kungiyar IS ta dawo da kai hare-haren bama-bamai a Bagadaza, inda ta kashe daruruwan mutane, a wani abu da ake gani martani ne kungiyar ke mayarwa game da kwace iko da wasu yankuna na kasar daga hannunta.