An kai hari kan masu jana'iza a Yemen ne bisa kuskure— Saudiya

Yemen Saudi
Bayanan hoto,

Wurin da aka kai hari kan masu taron jana'iza a Sanaa, babban birnin Yemen

Wani bincike da Saudiya ke jagoranta game da harin bom akan masu taron jana'iza a Yemen, ya nuna cewa jirgin yakin dakarun kawance da Saudiyan ke jagoranta ne ya kai harin bisa wasu bayanai marasa sahihanci.

Harin wanda aka kai a makon jiya, ya yi sanadiyar mutuwar mutane 140, da raunata wasu fiye da 500.

Hukumar da ke gudanar da binciken ta ce wani babban jami'in sojin Yemen ne ya bayar da bayanan masu kuskure, inda ya ce 'yan tawayen Houthi ne ke taro a lokacin, kuma akwai bukatar a dauki matakin gaggawa a kansu.

Masu binciken sun ce an kai harin ne batare da rundunar dakarun kawancen ta bayar da umurni na karshe akan shi ba.

Saudiya ta ce za a biya iyalan wadanda suka mutun diyya.