Barcelona ta doke Deportivo da ci 4-0

Spain

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rabon da Messi ya buga wa Barcelona tamaula tun ranar 21 ga watan Satumba a karawar da suka yi da Atletico Madrid

Lionel Messi ya ci kwallo a karawar da Barcelona ta ci Deportivo La Coruna 4-0 a gasar La Liga wasan mako na takwas da suka kara a Nou Camp.

Rahinha ne ya ci wa Barca kwallaye biyu kafin a je hutu, bayan da aka dawo Luis Suarez ya kara ta biyu, sannan Lionel Messi wanda ya dawo wasa bayan jinya da ya yi ya ci ta hudu.

Deportivo ta karasa karawar da 'yan wasa 10 a cikin fili bayan da aka bai wa Sanabria Ruiz jan kati sakamakon gula da ya yi wa Neymar bayan da aka dawo daga hutu.

Barcelona ta koma mataki na biyu a kan teburi da tazarar maki daya tsakaninta da Sevilla wadda ke kan teburi.