Syria: Ba'a cimma matsaya a kan yarjejeniyar tsagaita wuta ba

Asalin hoton, Getty Images
An tattauna muhimman batutuwa a tattaunawar
An kammala tattaunawar da ake akan Syria a birnin Lausanne da ke Switzerland tsakanin Amurka da Rasha da kuma manyan kasashen gabas ta tsakiya ba tare da cimma wata kwakwwarar manufa ba akan farfado da yarjejeniyar tsagaita wuta wadda za ta saukakawa fararen hular da ke birnin Aleppo mummunan yanayin da suke ciki.
Sai dai kuma sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya ce anyi tattataunawar ba bu wani boye-boye, sannan an kuma tattaunawa sabbin dabaru.
Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya bayyana sabbin dabarun a matsayin masu kayatarwa.
Haduwa ta gaba wadda za ayi tsakanin bangarorin da ke goyon bayan rundunonin soji da ke hamayya da juna a Syria zata kasance a ranar litinin mai zuwa.
Amma kafin nan, Mr Kerry zai tuntubi ministocin harkokin wajen Birtaniya da Faransa da Jamus a London.