Ban Ki-Moon ya ce al'ummar Haiti na bukatar agajin gaggawa

Ban Ki-Moon ya ce ana bukatar kayan agaji a Haiti
Bayanan hoto,

Ban Ki-Moon na ziyara a Haiti

Sakatare janar na majalisar dinkin duniya, Ban Ki-Moon, na ziyara a Haiti domin ya ja hankalin kasashen duniya akan irin barnar da mummunar guguwar nan da aka yiwa lakabi da Matthew ta haddasa.

Mr Ban ya samu tarbar firaminista Enex Jean-Charles, inda daga nan sai su ka hau jirgi mai saukar ungulu domin ziyarar wajen a kudancin birnin Les Cayes.

A farkon makon nan ne Mr Ban ya ce akwai bukatar agajin gaggawa mai yawan gaske daga kasashen duniya, bisa la'akari da yadda garuruwa da kauyuka suka shafe, yayinda mutane miliyan daya da rabi ke bukatar taimakon gaggawa daga sauran al'umma.

Ana kuma kara kamuwa da cutar amai da gudawa a Haitin saboda rashin tsaftataccen ruwan sha.