An kwace garin Dabiq daga hannun IS

'Yan tawayen sun mazaya zuwa Dabiq ranafr Asabar

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan tawayen sun mazaya zuwa Dabiq ranafr Asabar

Wasu 'yan tawaye da ke samun goyon bayan Turkiyya sun kwace garin Dabiq, mai matukar muhimmanci daga hannun 'yan kungiyar IS.

Kwamandojin 'yan tawayen da kuma kungiyoyin da ke sa ido kan IS sun tabbatar da kwace garin.

'Yan tawayen sun kwace ikon garin Dabiq ne bayan "Mayakan IS sun janye daga cikinsa", in ji kungiyar kare hakkin dan adam ta Syrian Observatory for Human Rights wacce ke da hedikwata a London.

Garin dai na da matukar muhimmanci a wurin 'yan kungiyar ta IS saboda ikirarin da suke yi cewa wani fagen-daga ne na mutanen da.

Kwace garin na cikin yunkurin da 'yan tawayen Syria ke yi na kawar da IS daga wuraren da ta mamaye.

Ahmed Osman, kwamanda kungiyar 'yan tawaye ta Sultan Murad, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ranar Lahadi cewa kungiyarsa ta sake kwace kauyen Soran da ke kusa da Dabiq.

Dabiq dai na da nisan kilomita 10 daga kan iyakar Syria da Turkiyya.

A watan Agusta ne dai Turkiyya ta kaddamar da gagarumin hare-hare domin kawar da masu tayar da kayar baya daga kan iyakarta.