China za ta aika da 'yan-sama-jannati zuwa tasharta da ke sama

'Yan-sama-jannatin za su tashi ne daga tashar tauraron dan adam da ke arewacin kasar.
Bayanan hoto,

'Yan-sama-jannatin za su tashi ne daga tashar tauraron dan adam da ke arewacin kasar.

Kasar China na shirin harba roka dauke da 'yan-sama-jannati biyu zuwa tasharta da ke sararin samaniya ranar Litinin.

Jami'an gwamnatin kasar sun ce 'yan-sama-jannatin za su tashi ne daga tashar tauraron dan adam da ke arewacin kasar.

An tsara cewa za su kwashe kwana 30 a cikin tashar mai suna Tiangong 2 , inda za su rika aunawa ko akwai yiwuwar dan adam ya rayu a wurin.

Ana yi wa wannan shiri da ma wanda ya gabace shi kallon wata alama da ke nuna cewa akwai yiwuwar aika wata tawaga zuwa duniyar Wata ko ta Mars.

'Yan-sama-jannatin da za su yi tafiyar su ne Jing Haipeng, mai shekara 49, wwanda sau biyu yana zuwa tashar ta sararin samaniya da kuma Chen Dong, mai shekara 37.