An kama jagoran dalibai a Afirka ta Kudu

Jocob Zuma
Bayanan hoto,

Shugaba Jocob Zuma na Afika ta Kudu

'Yan sanda a Afika ta Kudu sun kama daya daga cikin shugabannin dake jagorantar zanga-zangar dalibai a kasar.

Kungiyar dalibai a kasar ta ce 'yan sanda sun kama Mcebo Dlamini ne a dakinsa a jami'ar Witwatersrand dake Johannesburg.

Mista Dlamini ya na cikin wadanda ke gaba-gaba a fafutukar neman a rage kudin makaranta, abin da har yasa daliban yin arangama da 'yan sanda a lokuta da dama.

Dalibai a jami'o'i a fadin kasar ne suka rika yin zanga-zanga domin ganin gwamnati ta mai da karatu kyauta a kasar.