Gwamnatin Kuwait ta yi murabus

Majalisar Dokokin kasar Kuwait
Sarkin Kuwait ya rusa majalisar dokokin kasar, bayan gwamnatin kasar ta yi murabus.
Gwamnatin ta yi murabus ne yayin da ake ci gaba da samun fargaba game da tattalin arziki da tsaron kasar.
Faduwar farashin mai a kasuwannin duniya ta shafi tattalin arzikin kasar sosai, abin da ya sa aka samu karin kudin da gwamnati ke kashewa akan tallafin farashin mai, da kuma rage yawan garabasar da mutane ke samu.
Za a gudanar da sabon zabe a kasar cikin watanni biyu masu zuwa.