Dakarun Iraqi na kokarin kwato birnin Mosul

Dakarun Iraqi na dunfarar birnin Mosul

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shekaru biyu kenan da mayakan IS suka karbe iko da birnin Mosul.

Sojoji na cigaba da kokarin kwato birnin Mosul daga hannun masu tayar da kayar baya na kungiyar IS a kasar Iraqi.

Firaiministan Iraqi, Haidar al-Abadi ne ya sanar da hakan, a inda ya ce ana fafatawa a babbar matattara ta karshe ta mayakan kungiyar ta IS.

Mayakan Kurdawa na Peshmerga ne ke jagorantar samamen, a sa'o'insa na farko, suna dannawa kauyuka dake gabashin Mosul, suna kuma share wa dakarun Iraki hanya.

Wani kwamandan sojin Kurdawa, ya ce dakarun na Peshmerga sun dan rage hanzari, sabo da bama-bamai kirar gida dake warwatse a kan manyan hanyoyi, da fagage, kazalika IS na cigaba da kai hare-haren bama-bamai din mota na kunar bakin wake.

Fiye da shekaru biyu kenan da mayakan IS suka karbe birnin na Mosul.

Yanzu haka kuma kungiyar ta rasa iko da yawancin wuraren da ta mamaye a baya.

An dai girke kusan dakaru da mayakan sa-kai 300,000 a kewayen birin, inda hankalin gwamnatin Iraqi da jiragen yakin Amurka ya karkata.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

An kuma kiyasin akwai mayakan IS kusan 8000 a cikin birnin.

Sai dai Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa matuka, game da makomar fararen hula miliyan daya da rabi da ke cikin birnin.

To amma shugaban yankin Kurdawa na Iraqi, Masoud Barzani, ya ce mayakansa sun samu ci gaba, sai dai ya yi gargadi game da mayar da Mosul tamkar Aleppo.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana hanzartawa domin kammala samar da sansanoni na gaggawa, domin tsugunar da fararen hula wadanda gumurzun neman iko da Mosul din ka iya rabawa da muhallansu.

Jami'ar tsare-tsaren ayyukan jin kan bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Lise Grande, kenan tana cewa, a halin yanzu mun damu matuka kan tsaron lafiyar fararen hula dake cikin birnin, suna cikin hadari, za a yi rutsawa da su a musayar wuta, mun fahimci kungiyar IS tana da tarkunan bam a birnin'.

To sai dai jami'ar ta ce kungiyoyin agaji na da isassun tantuna da kayakin masarufi domin tallafa wa mutane har dubu dari hudu