Sarki daya tilo da ya rage a Rwanda ya rasu

Daya daga cikin tsaffin masarautun gargajiya a Rwanda

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sarki Kigeli na biyar ya dade da barin kasar Rwanda.

Sarki daya tilo da ya rage a kasar Rwanda, wato Sarki Kigeli na biyar, ya mutu a Amurka, yana da shekara tamanin a duniya.

Tun a shekarar 1959 yake matsayin sarkin Rwanda, har zuwa shekarar 1961 a lokacin da aka tarwatsa masarautar kasar.

Ya kuma tsere daga kasar shekara daya bayan nan, a lokacin da aka yi wani juyin mulki da gwamnatin Belgium da ta mulki kasar ta mara wa baya.

Ya zauna a kasashen Afurka da dama, daga bisani kuma ya samu matsuguni na dindindin a kusa da birnin Washington din Amurka.

A baya dai gwamnatin Rwanda ta sanar da shi cewa, tana maraba lale da shi a duk lokacin da ya so komawa gida, amma fa ba a matsayin sarki ba.