Harin bam ya kashe'yan gida 14 a Aleppo da ke Syria

Birnin Syria da ke Aleppo

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Masu aikin agaji, White Helmets sun ce an jefa bama-bamai da dama cikin 'yan sa'o'i 24 a birnin Aleppo.

Jami'an aikin agaji a Syria, da aka fi sani da White Helmets, sun ce 'yan gida daya su 14 sun rasu, sanadiyyar wani hari ta sama da aka kai a gabashin birnin Aleppo.

Cikin wadanda suka mutu har da jarirai biyu da ba su fi makwanni shida da haihuwa ba, da kuma wasu yara kanana shida 'yan kasa da shekara takwas.

A ranar Litinin ne dai iyalan suka mutu, a yankin al-Marja da ke cikin birnin, sakamakon wani hari daake tsammanin jiragen yakin Rasha ne suka kai.

Wani mazaunin Aleppo, ya shaida wa BBC cewa, birnin ya sha fama da bama-bamai cikin 'yan sa'o'i 24, inda har ya kai ga girgizar kasa.

Babbar jami'ar Kungiyar Tarayyar Turai, watau EU, kan tsarin manufofin kasashen waje, ta ce akwai yiwuwar za a kara wa'adin tankunkumin da aka kakabawa Syria.

Da ta ke magana a taron ministocin harkokin wajen kasashen da ke kungiyar ta EU, a Luxembourg, Federica Mogherini, ta ce, karin wasu takunkumi kan gwamnatin Syria karkashin ikon Bashar Assad da ke da goyon bayan gwamnatin Rasha, ba ya cikin lissafinsu a yanzu.

Daruruwan mutane ne suka mutu a Aleppo, sakamakon hare-hare daga dakarun Rasha da kuma na gwamnatin Syria, tun bayan rushewar wata yarjejeniyar tsagaita wuta a watan da ya gabata.

Dakarun dai sun jaddada cewa suna kai wa 'yan ta'adda ne kawai hari.