Za a rusa gidan da aka haifi Hitler

Gidan da aka haifi Adolf Hitler

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ana tattauna batun rusa gidan da aka haifi Adolf Hitler, wanda aka maida gidan saukar bakin gwamnati

Ana shirin rusa gidan da aka haifi Adolf Hitler da nufin hana wurin zama wata matattara ga masu akidar Nazi.

Ana ta muhawara game da makomar gidan a Austria, inda ra'ayoyi suka bambanta a kan a rusa shi ko kuma a sauya tsarinsa.

Takaddamar ta kara ta'azzara ne dai bayan da wanda ya mallaki gidan ya ki sayar da shi.

Sai dai kuma jaridar Die Presse ta kasar Austria ta bayar da rahoton cewa Ministan Cikin Gida Wolfgang Sobotka ya ce wani kwamitin kwararru ya yanke shawarar cewa a rusa gidan.

Jaridar ta kara da cewa za a yi amfani da sabon ginin da za a yi a wurin don gudanar da harkokin mulki ko kuma bayar da agaji.