Rasha za ta dakatar da kai hare-hare birnin Aleppo

Za a tsagaita wuta ne na tsawon sa'o'i 8

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Rasha ta ce za ta dakatar da kai hare-hare Aleppo

Rasha ta sanar da cewa ta tsagaita wuta a hare-haren da ta ke kaiwa birnin Aleppo na Syria, domin a samu dama kai kayan agaji.

Hukumomin Rasha sun ce za a dakatar da kai hare-hare a ranar Alhamis har tsawon sa'o'i takwas.

Ma'ikatar tsaron kasar ta ce an amince da tsagaita wutar ne, sabo da fararen hula da 'yan tawaye su samu damar ficewa.

Sanrwar dakatar da kai hare haren dai ta zo ne bayan wani hari ta sama ya janyo mutuwar mutane 14 yan gida daya a birnin na Aleppo.

Wani jami'in ma'aikaar harkokin tsaron Rasha Sergei Rudskoy shi ne ya bayyana matakin na tsagaita wutar ranar Litinin.

Mr. Rudskoy ya ce Rasha na aiki domin kawo karshen rikicin da ake fama da shi a Aleppo, to amma ya ce za a iya shafe lokaci mai tsawo kafin a cimma yarjejejeniya kan duka batutuwan da suka shafi yakin.