Nigeria: Ba a kula da sauran matan da BH ta sace

Wasu daga cikin iyayen 'yan matan Chibok

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu na ganin cewa sauran mata da 'yan matan da Boko Haram ke sacewa, ba a daukar nauyin su kamar yadda aka yi wa 'yan matan Chibok.

Masu sharhi sun fara tsokaci game da irin kulawar da ake baiwa 'yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta mika wa gwamnatin Najeriya.

Gwamnatin dai ta dauki alhakin kula da karatun 'yan mata 21 da Boko Haram ta saki a makon jiya da ma wadda 'yan kato da gora suka kwato a farkon wannan shekarar.

Sai dai wasu na ganin gwamnatin ta fi ba da fifiko wajen wadannan 'yan mata na Chibok fiye da sauran mata da kuma yaran da aka kwato daga hannun 'yan ta'addan, wadanda a mafi yawancin lokaci ana kaisu sansanin 'yan gudun hijira ne.

Dacta Husaini Abdu shugaban kungiyar PLAN International mai zaman kan te, da ke yaki da talauci a Najeriya, ya kuma shaidawa BBC cewa an siyasantar da batun 'yan matan na Chibok.

Saboda yadda akai ta yada abun da kuma fifikon da aka nuna akan su, da fafutukar da kungiyoyi a ciki da wajen Najeriya suka shiga gangamin matsawa gwamnati lambar kubutar da su daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram.

Ya kara da cewa ko a ganganmin neman kujerar shugaban kasa da aka yi a kasar, batun 'yan matan Chibok na daga cikin batutuwa mafi muhimmanci da gwamnatin mai mulki ta yi wa 'yan Najeriya alkawarin kubutar da su da tabbatar da tsaro.