Dakarun Iraqi na ci gaba da dannawa birnin Mosul

Jerin gwanon tankokin yaki a Mosul

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shekaru biyu kenan birnin Mosul na hannun 'yan IS.

An shiga rana ta biyu da fafatawar da ake yi a birnin Mosul din Iraqi, inda dakarun kasar da mayakan na Kurdawa ke ci gaba da dannawa dan sake kwato shi daga hannun masu tada kayar baya na kungiyar IS.

Mai magna da yawun sojin Amurka tabbatar da kawancen kasashen waje sun kai hare-hare maboya 'yan IS a birnin na Mosul kafin su fara fafatawa ta kasa.

Masu sharhi kan al'amura sun ce kawo yanzu dakarun kawancen na samun nasara a kokarin da suke yi.

Tun da fari IS ta fitar da wani faifan bidiyo na farfaganda, da ya nuna mazauna Mosul na ta gudanar da harkokin su na yau da kullum ba tare da harin da sojojin ke kaiwa ia same su ba.

Sara Case jami'a ce a hukumar International Rescue Comiitee ta shaidawa BBC su na kokarin tanadar matsugunin fararen hular da ka iya rasa muhallansu.

Sara tace su na sa ran fiye da mutane dubu dari biyu za su tsere daga gidajensu cikin makwanni masu zuwa, idan aka ci gaba da fafatawar da ake yi, za kuma su iya kaiwa miliyan guda cikin watanni masu zuwa.

A nata bangaren Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa matuka, kan halin da fararen hula za su riski kan su a ciki.