Amurka: Kalaman batsa ba halin Donald Trumb ba ne

Melania dai tana takaicin batun da ake yi cewa mijinta ya yi lalata da wata mace

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Donald Trump ya yi kalaman batsa ne a 2005

A fakaice uwargidan dan takarar shugabancin Amurka Donald Trump, ta kare mijin na ta, a kokarin rage sukar lamirinsa da ake yi game da kalaman batsa da ya yi.

A wata hira da gidan talabijin din kasar, Melania Trump ta roki Amurkawa su yafewa Misis Trumpy din kamar yadda ita ma ta yi.

Tace a ganin ta kalaman kaifafa ne kuma ba su dace ba, ya ba ta hakuri kan hakan, ya nemi afuwa ta kuma na yafe masa sun ci gaba da harkokin mu.

Melania ta kara da cewa irin wadanna kalamai ba dabi'ar Mista Trump ba ce, ta kara da cewa ba ta amince matan su na zarginsa da aikata lalata da su ba.

Bullar faifan bidiyon kalaman batsa da ya yi amfani amfani da su akan mata tun a shekarar 2005 dai ya janyo masa koma baya ta fuskar siyasa.

Hakan kuwa ya janyo abokiyar hamayyarsa ta jam'iyyar Democrats Hillary Clinton ta ke kara samun goyon baya ba a Amurka kadai ba har ma a wasu kasashen duniya.