Fari ya janyo karancin abinci a Madagascar

Asalin hoton, Getty Images
Fari ya janyo karancin abinci a Madagascar
Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutum 600,000 ne ke fama da matsanancin rashin abinci a kudancin kasar Madagascar.
Tsibirin teku na kudancin kasar na fama da fari tsawon shekara uku a jere. Amfanin gona ya lalace a yankin Androy.
Annobar sauyin yanayi ta El nino ta auka wa Madagascar, lamarin da ya haddasa karancin ruwa a kudancin Afirka.
Lamarin ya tilasta wa wani bangare na jama'ar kasar sayar da kadarorinsu da yin kaura wasu kuma sun dirfafi cin 'ya'yan itatuwan da ba a saba ci ba don su tsira.
Wasu manoma a kasar sun fara kokarin noma kayan abincin da ba sa bukatar ruwa sosai irin su Gero.