Mayakan Al-Shabab na gumurzu da sojojin Somaliya

Mayakan Al-shabab.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Mayakan Al-shabab sun kai hari garin Afgoye da ke kusa da Mogadishu babban birnin Somaliya.

Ana gwabza fada a Mogadishu, babban birnin Somaliya, tsakanin mayakan Al-Shabaab da dakarun gwamnati masu samun goyon bayan kungiyar Tarayyar Afrika, watau AU.

Mazauna birnin sun shaida wa BBC cewa suna ta faman neman mafaka daga harsasan da aka yi ta harbawa har cikin dare.

Wani jami'in kasar Uganda da ke wakiltar kungiyar AU a kasar ta Somalia ya ce an kora mayakan, amma ba a tabbatar da hakan ba tukunna.

Wasu da lamarin ya afku a gabansu sun ce mayakan Al-Shabaab sun dirar wa garin Afgoye ne a ranar Talata.

Harin kuma ya soma ne bayan da bam ya tashi awata mota, wanda mazauna garin suka ce ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan sanda akalla hudu.

Gwamnatin Somaliya da kungiyar AU sun kara tura dakarun soji domin taimaka wa wadanda ke kasa.

Garin Afgoye dai na da muhimmanci sosai, ganin kusancin sa da Mogadishu babban birnin kasar, kuma a nan ne manyan tituna biyu kacal da birnin ke da su suke.

Ana shirin gudanar da zaben majalisar dokokin Somaliya, kafin zaben shugaban kasa da za a yi a watan Nuwamba, amma kuma shirye-shiryen na fuskantar matsalolin tsaro.