FA ta tuntubi Mourinho kan alkalin wasa Taylor

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mourinho ne ya maye gurbin Louis van Gaal a Manchester United

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tuntubi Jose Mourinho, kan maganar da ya yi cewar Anthony Taylor zai busa wasan Manchester United da Liverpool da gumin goshi a ranar Litinin.

Mourinho ya ce wasu da gangan suke yin kokarin saka matsi a kan alkalin wasan, wanda ke mara wa kungiyar Altrincham baya.

A dokar hukumar kwallon kafa ta Ingila, ba ta amincewa mai horar da kungiyar da ke buga gasar Premier ya yi magana kan alkalin wasa gabannin karawa ba.

Hukumar ta bai wa Mourinho zuwa ranar Juma'a domin ya fayyace abin da yake nufi wanda za ta yi amfani da shi wajen yanke hukunci.