Saudiya: An zartar da hukuncin kisa kan wani Yarima

Sarki Salman bin Saud

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sarki Salman ya yi watsi da korafe-korafen kasashen Yamma kan hukuncin kisa da kasar ke yawan aiwatarwa

An zartar da hukuncin kisa a kan wani Yarima a masarautar Saudiyya, bisa samun shi da laifin harbe wani mutum shekaru uku da suka gabata a birnin Riyadh.

Ma'aikatar cikin gidan kasar ta ce an zartar da hukuncin kan Yarima Turki bin Saud al-Kabir, bayan samun shi da laifin harbe wani dan kasar, Adel bin Suleiman bin Abdul Karim Mohaimeed yayin wata rigima tsakaninsu.

Babu wabi cikakken bayani da aka yi kan yadda aka zartar da hukuncin a kan Yariman, amma dai yawancin mutanen da ake aiwatar da hukuncin kisa a kansu a kasar, ana fille musu kai ne.

Dangin wanda yariman ya kashe, sun ki amincewa da tayin ba su diyyar kudi, inda suka bukaci a yi adalci kan wanda ya hallaka dan uwan nasu kawai.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch, ta ce fiye da mutane dari masarautar Saudiya ta aiwatar da hukuncin kisa a kansu cikin shekarar nan.

Ba kasafai ake aiwatar da hukuncin kisa ga 'ya'yan masarautar Saudiyya ba.