Za a yi taro dan magance matsalar Libiya

Dakarun Libiya a bakin aiki.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Mu'ammar Gaddafi Libiya ta samu kan ta da tabarbarewar tsaro.

A jamhuriyar Nijar idan an jima ne ministocin harkokin waje na kasashe makwabtan kasar Libiya za su yi wani taro a Yamai babban birnin kasar domin tattaunawa a kan halin da ake ciki a kasar Libiya.

Kasashen makwabtan Libiya na son bada tasu gudummuwar kan kokarin da kasashen duniya ke yi don samar da zama lafiya a kasar.

Kasashe irin su Chadi, da Masar, da Algeria kuma Sudan.

Sannan kuma kungiyoyi masu zaman kan su na kasashen waje su ma za su halarci taron.

Tun dai bayan hambarar da gwamnatin shugaba Mu'ammar Gaddafi a lokacin guguwar sauyi da ta kada a kasashen labarawa, kasar ta Libya ta shiga cikin tsaka mai wuya.

Ta fuskar tsaro da kwararowar kungiyoyin 'yan ta'adda da 'yan cirani da 'yan gudun hijira.

Haka kuma aka sa mu rarrabuwar kawuna ta fuskar siyasa, lamarin da ya kai ga samar da gwamnatoci guda biyu a Libiyar.

Daya kasashen yammacin duniya su na mara mata baya, da kuma gwamnatin 'yan tawaye.