Ɗan gidan Saro-Wiwa ya mutu

Ken Saro-Wiwa Jr ya mutu yana da shekara 47
Ken Saro-Wiwa jr, mai shekara 47 wanda ɗa ne ga mai rajin Kare Mahallin nan na yankin Naija Delta a Najeriya, Ken Saro-Wiwa, ya mutu, a London.
Gwamnatin tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya, Janar Sani Abacha ce dai ta kashe Mahaifin Ken Saro-Wiwa jr, wato Ken Saro-Wiwa sr.
Al'amarin kisan nasa wanda ya janyo kace-nace a fadin duniya, ya haddasa korar Najeriya daga Kungiyar Kasashe Rainon Burtaniya.
Shi dai Saro-Wiwa ya jagoranci Kungiyar Cigaban Al'ummar Yankin Ogoni da aka fi sani da Mosop, a inda ya zargi kamfanin mai na Shell da lalata musu mahalli.
Ken Saro-Wiwa Snr dai ya rasa ransa ne a lokacin mulkin Janar Sani Abacha a 1996