Filato: An haramta mallakar makamai babu lasisi

Gwamnan jihar Filato Barista Simon Bako Lalong

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Jihar Filato ta sha fama da rikicin addini da kabilanci.

Gwamnatin Jihar Filato a Nigeria ta yi tayin afuwa ga mutanen da suka mika makamansu cikin ruwan sanyi, a wani mataki na tabbatar da dorewar zaman lafiya a Jihar.

Gwamnan Jihar ne ya yi wannan kira ga duk wadanda suke mallakar makaman ba tare da lasisi ba.

Jihar Filato dai a baya ta sha fama da rikice rikice masu nasaba da addini da kuma kabilanci.

Inda da zarar rikici ya barke tsakanin al'uma sai a fara dauko makamai, ana hallakawa da jikkata wadanda ba su san hawa ba bare sauka ba.

Mai magana da yawun gwamnatin Jihar Mr Dan Manjan, yace dalilin gwamnati na daukar wannan mataki, shi ne ganin zaman lafiya ya fara dorewa tsakanin al'uma bai kamata a zuba ido mutane su mallaki makaman da za su iya cutar da wasu da shi ba.