Amurka: Trump ba zai amince da shan kaye a zabe ba

Asalin hoton, Getty Images
Wannan ita ce muhawara ta karshe tsakanin 'yan takarar.
A muhawara ta karshe tsakanin 'yan takarar shugaban kasar Amurka na Jam'iyyun Republican da Democrat, Mista Donald Trump ya ki bada tabbacin ko zai amince da duk yadda sakamakon zaben zai kasance.
Mista Trump ya yi ta nanata cewa ana kokarin yi masa magudi, dan haka zai jira har lokacin zaben ya ga abinda zai faru.
A nata bangaren Misis Clinton ta ce ta kadu matuka, da dantakarar shugaban kasa a Amurka ya dauki irin wannna mataki, ta kuma zargi Mista Trump da janyowa Dimukradiyyar Amurka koma baya.
'Yan takarar sun shafe tsahon sa'a daya da rabi su na sukar juna, da kaifafan kalamai.
Misis Clinton ta zargi Donald Trump da koda shugaba Vladimir Putin na Rsha, inda ya ke cewa zai yi amfani koyi da manufofin sa idan ya ci zabe.
Ya yin da shi kuma ya zarge ta da shirya masa makarkashiya a lokacin yakin neman zabe.