Faransa da Jamus sun soki Rasha kan rikicin Syria

Francoise Hollande da Angela Merkel

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugannin biyu sun ce lokaci ya yi da Rasha za ta tsame hannun ta daga cikin rikicin Syria.

Shugabannin kasashen Jamus da Faransa sun soki Rasha kan ruwan bama-baman da ta ke a birnin Aleppo na Syria.

Bayan tattaunawar da suka yi da shugaba Vladimir Putin a birnin Berlin, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kira matakin da Rashar ke dauka da cewa rashin imani ne.

Ya yin da shugaba Francois Hollande ya ce Rashar ta aikata laifin yaki.

Ya kuma ce ba zai taba yiwuwaa samu damar ganawa da Mista Putin ba tare da an kawo batun halin da ake ciki a birnin Aleppon Syria, a kuma bayyane ta ke an aikata laifukan yaki, idan har za a duba abinda ke faruwa a Aleppo.

Sai dai kuma ya ce da alama shugaba Putin a shirye ya ke dan kara wa'adin dakatar da bude wuta a birnin Aleppo.

Nana gaba a yau ne kuma tsagaita wutar za ta fara aiki a hukumance, wadda manufar ta shi ne 'yan tawaye su samu damar ficewa daga yankin, tare da fararen hula da suka jikkata.