Ba zan sauya salon wasana ba —Guardiola

Asalin hoton, Rex Features
Pep Guardiola ya ce ba shi da niyyar sauya salon wasa
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce ba zai sauya salon wasan kungiyar ba duk da shan kashin da suka yi a hannun Barcelona da ci 4-0.
A wasan dai, Lionel Messi ya zazzaga wa City kwallaye uku rigis, yayin da alkalin wasa ya bai wa mai tsaron raga Claudio Bravo jan kati bayan da ya taba kwallo a wajen da'irarsa.
Guardiola ya ce,"Ba za mu sauya salon wasanmu ba. Zan ci gaba da aiwatar da tsarin da nake bi na yanzu har karshen wa'adina na koci."
Yanzu dai Barca kan gaba a rukunin C na gasar cin kofin zakarun turai inda take da maki tara, kuma tana gaban City da maki hudu.