Nigeria: An sace wani babban malamin addinin Musulunci

Barayin sun bukaci a biya kimanin N10m

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Barayin sun bukaci a biya su wasu kudade kafin su sake shi

Wadansu barayin mutane sun sace wani fitaccen malami da ke jihar Sokoto ta Arewacin Najeriya.

An yi awon gaba da Malam Muhammad Lawal Maidoki, wanda ke aiki a hukumar raya kogin Rima ta jihar Sokoto a ranar Laraba kan hanyar Minna zuwa Kaduna.

Barayin sun sace malamin ne tare da matarsa da matar kaninsa yayin da suka sallami direbansa.

Sai dai wata majiya a danginsa ta shaida wa BBC cewa barayin suna tattauna da barayin domin kubutar da shi.

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta ce tana aike da takwararta ta jihar Neja domin ceto mutanen.

Najeriya dai ta yi kaurin-suna wajen yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, inda ko a baya-bayan nan sai da barayin mutanen suka sace matar shugaban babban bankin kasar, Godwin Emefiele.

Tun da farko mun rawaito bisa kuskure cewa an sace shi ne a brinin Sokoto, da fatan za a yi mana afuwa.