An yi kira ga Rahama Sadau da kada ta amsa gayyatar Akon

Rahama na matukar sha'awar fina-finan Indiya
Bayanan hoto,

Rahama ta ji dadin gayyatar da Akon ya yi mata

Fitaccen Malamin addinin Musulincin nan na Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi kira ga jarumar Kannywood, Rahama Sadau da kada ta amsa gayyatar da wasu fitattun mawaka suka yi mata zuwa Amurka.

A wata budaddiyar wasika da ya wallafa a shafinsa na Facebook, wadda kuma ya bukaci a mika sakonsa ga jarumar, ya ce: "Ke dai Musulma ce kuma mu Musulinci shi ne abin dubawa a gare mu."

Sheikh Daurawa ya kuma bukaci jarumar da ta yi aure domin a cewarsa shi ne "ya fi dacewa da ita".

Shahararren mawakin nan Akon da takwaransa Jeta Amata ne suka yi gayyaci Rahama Sadau zuwa birnin Los Angeles na Amurka domin ta halarci wurin da suke hada sabon fim dinsu na Hollywood.

Sun ce suna so su "karfafa mata gwiwa" bayan korar da aka yi mata daga fina-finan Kannywood saboda an same ta da laifin rashin da'a sakamakon rungumar da ta yi wa Classiq a bidiyon wakar da suka yi tare.

Sai dai Sheikh Daurawa ya ce ya kamata ta yi tunani kan wannan gayyatar, wacce tuni ta riga ta amsa.

Asalin hoton, Aminu Daurawa

Bayanan hoto,

Sheikh Daurawa ya ce ya kamata Rahama ta yi aure

Ita dai Rahama Sadau ta ce rungumar da ta yi wa Classiq ba laifi ba ne, tana mai cewa "ba zai yiwu na yi aiki ba tare da na taba wani ba."

Amma Malam Daurawa ya ce ya kamata "Ki sani cewa Musulinci addini ne wanda ya yarda da idan mutum ya yi kuskure a kira shi a gaya masa gaskiya, a tunatar da shi ayoyin Allah ko ya gyara."

Kawo yanzu Rahama ba ta ce komai ba kan wasikar ta Malam Aminu Daurawa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Akon ya ce yana son karfafa gwiwar Rahama Sadau

Asalin hoton, FINESSE ENTERTAINMENT

Bayanan hoto,

Ba wannan ne karon farko da take jawo ce-ce-ku-ce ba