Buhari ya nada jakadun kasashen waje

An zargi gwamnatin Buhari da yin tafiyar hawainiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An zargi gwamnatin Shugaba Buhari da yin tafiyar hawainiya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aika da sunayen mutum 46 zuwa ga majalisar dattawan kasar domin ta tantance su don zama jakadun kasar a kasashen waje.

Shugaban Majalisar Dattawan kasar Bukola Saraki ne ya karanta wasikar da shugaban ya aike wa 'yan majalisar ranar Alhamis.

Wasu daga cikin mutanen sun hada da Usman Bugaje, Yusuf Tugar, Musa Ibeto, Jamila Ahmadu-Suka, Sanata Olorunimbe Mamora, Nurudeen Mohammed, Suleiman Hassan da Pauline Talen.

Mutanen dai na cikin wadanda suka yi gwagwarmayar yakin neman zaben Shugaba Buhari.

A makon jiya ne dai mai dakin shugaban, Aisha Buhari, ta caccaki gwamnatin mijin nata saboda zargin da ta yi cewa ba a sanya 'yan jam'iyyarsu ta APC da dama a cikinta ba duk da wahalar da suka yi mata.

Sai dai babu tabbas ko mika wadannan sunaye na da alaka da kofare-korafen da Aisha Buhari ta yi.

Akwai bukatar majalisar dattawan ta amince da mutanen tukunna kafin a tura su kasashen da za su yi aiki.