'Yan sanda sun kama 'yan hamayya a Ivory Coast

'Yan kasar za su yi kuri'ar raba gardama

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan kasar za su yi kuri'ar raba gardama

'Yan sanda a Abidjan, babban birnin kasuwanci na Ivory Coast, sun kama shugabannin 'yan hamayya da dama, wadanda suka jagoranci wata zanga-zanga a kan wani sabon kudin tsarin mulki.

Wadanda aka tsaren sun hada da kakakin majalisa, Mamadou Koulibaly, da wasu sanannun 'yan siyasa.

Ba sa goyon bayan sabon kudin tsarin mulkin ne, wanda suka ce ya taimaka wa Shugaba Alassane Ouattara.

Kundin, wanda majalisar dokoki ta amince da shi, ya sauya dokokin da za su ba mutun damar takarar shugabancin kasa.

Nan gaba ne kuma, a karshen wannan wata, 'yan kasar za su yi kuri'ar raba gardama a kansa.