An kori manyan jami'an kwastam a Nigeria

Hukumar ta kwastam dai ta yi kaurin suna wajen karbar cin hanci da rashawa

Asalin hoton, Nigeria Customs

Bayanan hoto,

Hukumar ta kwastam dai ta yi kaurin suna wajen karbar cin hanci da rashawa

Hukumar yaki da fasa-kauri ta Najeriya ta kori manyan shugabanninta 29 saboda samunsu da laifuka.

Kakakin hukumar, Mr Wale Adeniyi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

A cewarsa, manyan jami'an na kwastam na cikin mutum 44 da hukumar ta sallama saboda laifin yin kafar-ungulu ga sha'anin tsaro da tattalin arzikin Najeriya.

Ya kara da cewa, "an yi wa jami'ai goma ritaya, sannan aka sallami mutum daya. Haka kuma an bai wa mutum hudu takardar gargadi, yayin da wasu mutum hudun -- wadanda bayan binciken da aka yi a kansu aka gano ba su da laifi -- aka wanke su."

Kakakin hukumar ta kwastam ya ce mutum hudun da aka kora suna da mukaman mataimakan shugaban hukumar, yayin da biyar kuma suke da mukaman mataimakansu.

A cewarsa, shugaban hukumar Kanar Hammed Ali (mai ritaya) ya bayyana karara cewa zai tunkari dukkan jami'an da ke da hannu wajen badakalar cin hanci da rashawa.

Hukumar ta kwastam dai ta yi kaurin suna wajen karbar cin hanci da rashawa, inda 'yan Najeriya ke kallon ta a matsayi daya daga cikin hukumomin da ke taimakawa wajen ta'azzarar matsalar tsaro saboda zargin ta da bari ana shigo da kayayyaki ba bisa ka'ida ba.