Pogba zai rika burge mutane —Mourinho

Pogba bai saba da salon taka leda na United ba

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Pogba bai saba da salon taka leda na United ba

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce dan wasan kungiyar Paul Pogba yana bukatar lokaci domin zaunawa da duga-duginsa a kulob din.

Dan wasan mai shekara 23, wanda kungiyar ta saya a kan £89m a watan Agusta, ya zura kwallaye biyu a dokewar da United ta yi wa Fenerbahce da ci 4-1 ranar Alhamis a gasar cin kofin Europa.

Pogba dai bai yi katabus ba a wasan da suka yi da Liverpool ranar Litinin inda suka tashi 0-0.

Mourinho ya ce, "Kwana biyu da suka wuce bai taka rawar gani ba a gasar Premier, amma kwana biyu bayan hakan ya zama abin alfahari. Yana bukatar lokaci. Kuma ina farin ciki da yadda yake murza leda".

Mourinho ya ce ya yi amannar cewa Pogba zai saba da salon murza leda daban-daban da kungiyar ke yi sabanin wanda ya saba da shi a lokacin yana Juventus.

Pogba, wanda bayan kammala wasan ya ce ya ji dadin yadda ya murza leda, yanzu ya ci kwallaye uku a wasanni 10 da ya yi wa United.